Dandalin Kannywood: Saukin kai gare ni – Inji Jaruma Nafisa Abdullahi

zttd

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood Nafisa Abdullahi hakika babbar jaruma ce da ta shafe shekaru da dama a masana’antar tare kuma da lashe kyaututtuka masu tarin yawa daga ciki da kuma wajen kasar nan.

Sai dai a lokuta da dama akan yi mata har ma da sauran jaruman na masana’antar kallon masu girman kai ko kuma nuna isa ga masoyan su, zargin da ita kuma jarumar ta karyata kai tsaye tare da jaddadawa masoyan ta cewar ita dai mai saukin kai ce.

Dandalin Kannywood: Saukin kai gare ni – Inji Jaruma Nafisa Abdullahi
KU KARANTA: Yadda ‘yan sanda suka far ma Nafisa Abdullahi a dakin ta na Otel

NAIJ.com dai ta samu cewa jarumar tayi wannan tsokacin ne a yayin wata fira da tayi da majiyar mu ta Weekly trust jim kadan bayan ta amshi kyautar ta ta gwarzuwar jaruma a fina-finan Afirika a birnin Landan.

A cewar ta da wannan zargin da ake yi mata dai sharri ne amma akwai lokutan da mutum yana wasu harkokin gaban sa ne ko kuma abubuwan duniya sun ishe shi to idan bai ba masoyan nashi cikakkiyar kulawa ba sai a dauka ko haka yake.

Daga karshe ne sai kuma ta kara tabbatar wa da magoya bayan ta cikakkiyar kaunar ta agare su tare da shan alwashin cigaba da kayatar da su a cikin fina-finan ta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a
For Promotion Of Your Music & Video Or Event On Our Websites, Call Or Whatsapp: +2348067385849

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *